Ana sasanta rikicin Sudan ta kudu

Fiye da mutane 100,000 rikicin ya shafa kai tsaye
Image caption Fiye da mutane 100,000 rikicin ya shafa kai tsaye.

Za'a ci gaba da kokarin sasanta rikicin Sudan ta Kudu ranar Juma'a.

Shugabannin kasashen gabashin Afrika za su hadu a Nairobi, babban birnin Kenya, da fatan dorawa kan tattaunawar da aka yi ranar Alhamis tsakanin shugabannin Kenya da Ethiopia da kuma shugaba Salva Kiir.

Babban jami'in agajin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu, Toby Lanzer, ya ce kasar ta shiga hali mafi tsanani tun bayan samun 'yancin kanta.

Ya ce akalla mutaen 100,000 ne rikicin ya shafa kai tsaye.

A yanzu haka dai ana ci gaba da yaki a arewacin kasar.

Karin bayani