An samu ci gaba wajen kawo karshen rikicin Sudan ta Kudu

Image caption Ana bukatar a dakatar da bude wuta nan take

Akwai alamun ci gaba don kawo karshen rikicin da ake a Sudan ta Kudu tsakanin gwamnatin Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar.

Masu shiga tsakani sun ce Mr Kiir a shirye yake a kawo karshen tashin hankalin da ake ciki a kasar

Sai dai Mr. Machar ya shaidawa BBC cewa ana bukatar sake tattaunawa nan gaba domin tabbatar da an tsagaita wutar da aka cimma.

Tun da fari shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya gargadi dukkanin bangarorin biyu.

Karin bayani