Yara 34 sun mutu a sansanin agaji na India

Image caption Talakawa Musulmi ne ke zaune a sansanonin.

Jami'ai a India sun ce akalla yara 34 ne suka rasu a sansanonin da aka kafa wa mutanen da suka guje wa rikicin da ya barke tsakanin Hindu da Musulmi a jihar Uttar Pradesh cikin watan Satumba.

Wani bincike da wani kwamitin gwamnati ya gudanar ya ce yaran sun mutu ne sakamakon ciwon Nimoniya da atini da kuma wasu cututtukan.

Ya musanta rahotannin kafofin watsa labarai cewar yaran sun mutu ne saboda ba su da kariya daga yanayin sanyi.

Rikicin na watan Satumba shi ne mafi muni da ya barke tsakanin al'umomin biyu a cikin shekaru 10.

Galibin wadanda suka tsere daga gidajen nasu dai Musulmi ne manoma mara sa galihu.