Jerin gwanon 'Yan adawa a Bangaladesh

Image caption Kawancen 'yan adawar na bukatar Firai Minista Sheikh Hasina ta yi murabus

A wani mataki na bijirewa haramcin da 'yan Sanda suka sanya musu ana tsammanin kawancen 'yan adawa a kasar Bangladesh za su gudanar da wani gagarumin Jerin gwano a babban birnin kasar Dhaka akan zabubbukan da za a gudanar nan da mako guda.

Kawancen 'yan adawar da Khaleda Zia ke jagoranta na bukatar Firai Minista Sheikh Hasina da ta yi murabus tare tare da kafa gwamnatin rikon kwarya kafin gudanar da zabe.

Gwamnatin ta yi watsi da bukatar 'yan adawar inda tace tsarin mulki ya tanadi dole a gudanar da zabubbuka.

'Yan sanda sun dakatar da hanyoyin sufuri domin su hana yin zanga-zangar, amma 'yan adawa sun ce ba gudu ba ja da baya.

Karin bayani