Lebanon: An yi jana'izar Chatah

Image caption An kashe Mr. Chatah a wani harin bom

An gudanar da jana'izar fitaccen dan siyasar nan da harin bam din da aka kai a cikin wata mota ya hallaka a tsakiyar babban birnin kasar Lebanoon Beruit.

An kashe Mohammad Chatah Tsohon Ministan kudi kuma tsohon jakadan Lebanon a Amurka a ranar Juma'ar da ta wuce tare da wasu mutane biyar.

A fakaice magoya bayansa na zargin gwamnatin Syria da kungiyar gwagwarmaya ta Hezbollah da kisan nasa, sai dai duka bangarorin biyu sun musanta hakan.

Abokan Mr. Chatah sun yi kira ga mutane da su fito domin yi masa jana'iza ta musamman.