Kalubalen tsagaita wuta a Sudan ta Kudu.

Mazauna Sudan ta Kudu
Image caption Mazauna Sudan ta Kudu

Ana cigaba da kai kawo domin kawo karshen tashin hankalin da ake yi a Sudan ta kudu.

Sai dai kuma duk da haka wani kakakin soja ya ce, a zahiri babu wata alamar tsagaita wuta.

Jagoran 'yan tawayen Riek Mashar ya ce, dakarunsa ne ke iko da mafi yawan arewacin kasar, sai dai kuma dakarun gwamnati sun ce, sun kwace iko da garin Malakal, kuma suna yi wa garin Bentiu na jihar Unity kawanya.

A halin da ake ciki dubban fararen hula na ci gaba da fakewa a ofisoshin majalisar Dinkin Duniya a sassan kasar.