Dakarun Machar na jerin gwano a garin Bor

Riek Machar
Image caption Riek Machar

A Sudan ta kudu dubban matasa magoya bayan jagoran 'yan tawaye Riek Mashar suna tunkarar garin Bor, mai matukar muhimmanci, wanda kuma shi ne babban birnin jihar Jonglei.

Yanzu haka dai dakarun gwamnati ne suke iko da garin na Bor, bayan sun kwace shi daga 'yan tawaye da tun farko suka kwace garin yayin da ake cigaba da fadan kabilanci a kasar.

Gungun matasan dai wani bangare ne na sojan sa kai 'yan kabilar Nuer.

Kuma kakakin shugaban kasar, Ateny Wek Ateng ya musanta cewa gwamnati tana shirin kai hari a garin Bentiu. Dakarun 'yan tawaye ne suka aukawa garin bayan jagoransu Riek Mashar ya yi watsi da tayin zaman lafiya.

Karin bayani