Zaben Yobe haramtacce ne- PDP

Bamanga Tukur
Image caption PDP ta bayyana zaben na Yobe haramtacce

Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta yi watsi da zaben shugabannin majalisun kananan hukumomi da aka gudanar a jahar Yobe a karshen mako

Sakamakon zaben dai ya nuna cewa sabuwar jam'iyyar adawa ta APC ce ta lashe dukkanin kujerun kananan hukumomin 17.

Jam'iyyar PDP wadda tun farko ta kauracewa zaben ta ce zaben haramtaccene, saboda an yi shi ne lokacin da jahar ke cikin dokar ta baci wanda ya sabawa dokokin kasar.

Hukumar zabe a Yobe dai ta bayyana cewa an gudanar da zaben lami lafiya kuma jama'a sun fito sosai.