An tsaurara tsaro a Rasha

Gwamnatin Rasha ta bada umarnin a tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen sama da tashoshin jiragen ƙasa bayan ɗan ƙunar baƙin wake ya kai hari a babbar tashar jirgin kasa ta garin Volgograd.

Lamarin dai ya haddasa mutuwar mutane akalla goma sha hudu, kuma wasu da dama sun jikkata.

Wannan hari dai ya zo ne a daidai lokacin da ake zirga-zirga sosai yayin da sabuwar shekara ke matsowa.

Wannan hari dai ya ƙarfafa fargabar cewa, za a kai karin hare-hare kafin wasannin Olympic.