'Yakin Sudan ta Kudu ya raba yara da iyalansu'

Yaran Sudan ta Kudu
Image caption Wasu yaran sun shaida yuadda aka kashe iyayensu

Kungiyar bada agaji ga kananan yara ta 'Save the Children' ta yi gargadin cewa ta yiwu yakin da ake a Sudan ta Kudu ya raba dubban yara da iyalansu.

Kungiyar 'Save the Children' ta kara da cewa yara da dama na dogaro da kansu ne a wurare daban daban na kasar.

'Wasu daga cikin yaran sun ga yadda aka kashe iyayensu da kuma lalata gidajensu'.

Wannan fadan dai ya barke ne kusan makonni biyu da suka gabata a babban birnin Kasar na Juba kuma ya bazu zuwa sasssan kasar da dama.

Akalla mutane dubu daya ne suka mutu

Sudan ta kudu dai ta samu 'yancin kaine daga Sudan a shekarar 2011 bayan an shafe shekara da shekaru ana rikici

Karin bayani