'Amurka ce babbar barazana a duniya'

Image caption Binciken ya nuna cewa sai an fi samun zaman lafiya da a ce akasarin mata 'yan siyasa ne

Wani bincike ya nuna cewa kashi daya bisa hudu na mutanen duniya sun yi ammanar cewa Amurka ce babbar barazana wajen samar da zaman lafiya a duniya.

Sai dai binciken, wanda da kungiyar WIN/Gallup International ta gudanar, ya kara da cewa Amurka ce kasar da ta fi shahara, inda mutane ke koma wa da zama.

Kazalika kungiyar ta ce mutanen da ta yi wa tambayoyi lokacin binciken sun bayyana cewa suna fatan shekarar 2014 za ta fi shekarar 2013 armashi.

Haka kuma sun ce za a fi samun zaman lafiya a duniya da a ce akasarin mata 'yan siyasa ne.