Boko Haram: An kashe mutane 12 a Borno

Image caption Jihar Borno na karkashin dokar ta baci

'Yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kashe mutane 12 tare da raunata wasu da dama a wani hari da su ka kaddamar a kauyuka biyu dake jihar Borno dake arewacin Nigeria.

'Yan Boko Haram din a kan babura sun kai hari a kan masu liyafar biki a kauyen Tashan-Alade a daren ranar Asabar sannan kuma a ranar Lahadi su ka kai hari a kauyen Kwajaffa.

Wanda ya shaida lamarin ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar 'yan Boko Haram a kan babura sun kaddamar da hare-hare a kan kauyukan kafin su kama gabansu.

A tsakiyar wannan shekarar, Shugaba Goodluck Jonathan ya kaddamar da dokar ta baci a jihohin arewa maso gabas, abinda ya tilastawa 'yan Boko Haram ficewa daga birnin Maiduguri su ka koma kan tsaunukan dake kan iyaka da kasar Kamaru.

A makon da ya gabata ne shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau a wani bidiyo yace kungiyarsu ce ta kadammar da hari a kan barikin sojoji dake garin Bama a jihar Borno.

Kawo yanzu dai hukumomin tsaro a Najeriyar ba su ce komai ba a kan faruwar al'amarin.

Karin bayani