Mukungubila ya dau alhakin hare haren Congo

Sojojin Congo
Image caption Gwamnatin Congo ta ce ita ke da iko da Kinshasa

Wani jagoran addini a jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ya shaidawa BBC cewa mabiyansa ne suka kai hare hare , a filin jirgin sama, da gida radiyo da talatbijin, da kuma wani sansanin soja, a Kinshasa, babban birnin kasar.

Mutumin, wanda ke ikirarin cewa shi mai bushara ne, Gideon Mukungubila, wanda kuma babban mai sukar lamirin shugaba Kabila ne, ya ce tashin hankalin ya faru ne a sakamakon cin fuskar da gwamnati ke yi.

Ya kuma musanta cewar an yi kokarin juyin mulki ne.

Gwamnatin Congon ta ce a yanzu ita ke da iko da Kinshasa, bayan an kashe akalla arba'in da shidda daga cikin maharan.

Karin bayani