Congo: Ana harbe-harbe a Kinshasa

Image caption Ana dade ana zaman dar dar a Congo

An ji karar harbe-harbe a wurare daban daban na babban birnin Jamhuriyar Demokradiyar Congo, ciki hadda shalkwatar gidan Talabijin da rediyo da kuma filin saukar jiragen sama na Kinshasa.

Matasa dauke da bindigogi da adduna sun yi garkuwa da manema labarai, kamar yadda kakakin 'yan sanda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Wani jami'in kwastam ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar 'yan bindiga sun diranma filin saukar jiragen sama, amma kuma ministan yada labaran kasar ya ce an shawo kan matsalar.

Kawo yanzu ba a san abinda ya janyo hare-haren ba.

Kafin gidan talabijin ya dauke daga watsa shirye shirye, 'yan bindiga biyu sun bayyana suna kalaman batanci a kan shugaba Joseph Kabila.

A shekarar 1997, dakarun kasar tare da goyon bayan na Rwanda suka hambarar da gwamnatin Mobutu Sese Seko suka saka Laurent Kabila wanda aka kashe kuma dansa Joseph Kabila ya dare kan mulki.

Karin bayani