Museveni ya yi wa Machar barazana

Image caption Machar ne shugaban 'yan tawaye a Sudan ta Kudu

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya yi barazanar daukar matakin soja a kan jagoran 'yan tawayen Sudan ta Kudu, Riek Machar.

Mr Museveni, ya ce idan dai Mr Machar ya ki amincewa da shawarar tsagaita wuta, babu wani zabi da ya rage ma kasashen gabashin Afrika da ya wuce na su murkushe shi.

An kashe mutane sama da 1,000 a rikicin kabilanci cikin makonni biyu da suka wuce.

Mr Museveni dai babban aboki ne na shugaba Salva Kiir, ya kuma tura sojoji zuwa Sudan ta Kudun.

Karin bayani