An samu tsaiko wajen kwashe makamai a Syria

Image caption Jinkirin wani komabaya ne ga Kasashen duniya dake cikin wannan aiki

Jirgin ruwan yakin daya kamata ace yana rakiyar tarin makaman syria masu guba zuwa wajen kasar na tsaye.

Jiragen ruwan Norway sun juya akalarsu bayan da manyan kwantenonin da zasu kwashi makaman suka gaza zuwa kwasar su a tashar jiragen ruwan Latakia.

A yanzu shirin da ake shine na kara sawa jiragen mai a Limassol kafin a sake komawa teku a 'yan kwanaki masu zuwa.

Jinkirin dai wani babban komabaya ne ga Kasashen duniya.

Da yawa da suke cikin wannan aiki na yiwa shirin kwasar makaman masu guba kallon wani abu da zai kawo tattaunawar zaman lafiya a Syria.

Idan aka kasa cimma abinda aka sanya a gaba, hakan zai nuna wahalhalun dake tattare da aiki a wata kasa dake canza iyakokinta akai akai koma da hadin kan da ake samu daga Shugaba Asad.

Karin bayani