Likita mai sayar da jarirai a China

Image caption 'Yan sanda sun damke Zhang Shuxia

Wata likita a arewacin kasar China ta amsa laifin satar jarirai daga asibitin da take aiki, tana kuma sayar da su ga wasu dillalai na wata kungiya mai safarar jarirai.

Ana zargin likitar, Zhang Shuxia ne da sace jarirai bakwai a kan wasu 'yan dubban daloli, bayan ta shaidawa iyayen jariran cewa an haifi yaran ne da wata nakasa.

An kamata ne jim kadan yayin da take dab da ritaya, lokacin da wata uwa jikinta bai bata ba, ta kai kara wurin 'yan sanda.

An gano shidda daga cikin jariran lami lafiya, amma daya ya rasu.

Akwai kuma wasu mutanen takwas da ake zargin suna da hannu wajen safarar jariran.

Karin bayani