An daure wasu 'yan jarida uku a Masar

Peter Greste
Image caption Mutanen da aka daure sun hada da tsohon wakilin BBC, Peter Greste

Hukumomin Masar sun yanke hukuncin daurin kwanaki sha biyar kan wasu manema labaru uku dake aiki da gidan talabijin na Aljazeera.

Wakiliyar BBC ta ce, wata sanarwa daga ofishin mai gabatar da kara na kasar ta Masar ta ce ana zargin manema labarun ne da shiga wata kungiyar 'yan ta'adda da aka haramta, suna kuma bada labaran karya da ke zubar da kimar kasar Masar.

Mutanen uku sun hada da tsohon wakilin BBC, Peter Greste, wanda dan kasar Australia ne.

Sai dai mahukuntan Masar din sun sako wani mai daukar hoto da aka kama tare da manema labarun uku.

Karin bayani