Faransa ta tabbatar da rage sojanta a Mali

Le Drian tare da sojin Faransa a Gao
Image caption Faransa ta ce za ta rage dakarunta dake Mali da kashi 60 cikin 100

Faransa ta bada karin haske kan yadda za ta yi matukar zabtare yawan dakarunta dake kasar Mali.

Ministan tsaron Faransa, Jean-Yves le Drian, wanda ke wata ziyara a kasar ta Mali, ya ce za a rage yawan sojojin da kashi sittin cikin dari, cikin watanni uku masu zuwa, inda za su bar sojoji dubu daya a can.

A cikin watan Janairun wannan shekara ne , sojojin Faransar suka fatattaki 'yan tawaye, wadanda suka kwace iko da arewacin Mali, amma duk da haka ana ci gaba da samun hare- haren 'yan tawayen.

Ya kamata a ce yawan dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Malin a yanzu ya kai dubu goma sha biyu; sai dai har ya zuwa yanzu adadin da ke can, bai kai rabin hakan ba.