An sako bafaranshen da aka sace a Kamaru

Image caption Fada Georges Vandenbeusch

Shugaban Faransa, Francois Hollande ya sanarda sakin wani fadan coci bafaranshe da aka sace a Kamaru a watan da ya gabata.

Fadan mai suna George Vandenbeusch, an sace shi ne a arewacin kasar dake kan iyaka da Nigeria inda aka saba yin garkuwa da mutane.

Kawo yanzu ba a san yadda aka sako shi, amma dai a lokacin da lamarin ya auku, kungiyar Boko Haram ta ce ita ce ta sace shi.

Shugaban Faransan, ya gode wa hukumomi a Kamaru da Nigeria da su ka taimaka wajen tabbatar da sakinsa.

Karin bayani