Shin me ya kai Namadi Sambo Kaduna?

Image caption Shugaba Goodluck Jonathan da mataimakinsa, Arc Namadi Sambo

Maitamakin Shugaban kasar Nigeria, Architect Namadi Sambo ya fara wata ziyara a jiharsa ta Kaduna, a daidai lokacin da wasu 'ya 'yan jam'iyyarsa ta PDP suka sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

Masu lura da al'amurra na ganin wannna batu na daga cikin muhimman abubuwan da mataimakin shugaban kasar zai mayar da hankali a wannan ziyarar ta sa.

Jihar ta Kaduna, inda Architect Namadi Sambo ya taba gwamna karkashin inuwar jam'iyyar PDP na da muhimmancin gaske a yunkurin da jam'iyyar PDP ke yi na ganin mulki bai kubce mata ba a zaben shekara ta 2015.

A makon da ya wuce ne wasu kusoshin jam'iyyar PDP karkashin tsohon shugaban jam'iyyar na jiha, Alhaji Audi Yaro Makama su ka koma jam'iyyar adawa ta APC.

Masu sharhi dai na gannin cewar sauya shekar babban koma baya ne da mataimakin shugaban kasar wanda wasu ke kallo a matsayin baida karfin fada aji a fagen siyasar arewacin Nigeria.

Sai dai wasu daga cikin na hannun daman mataimakin shugaban kasar ya ce ziyarar ta sada zumunci ce.

Karin bayani