'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun kwace Bor

Image caption Dubban mutane sun rasa matsugunansu a Sudan ta Kudu

Dakarun dake adawa da gwamnatin Sudan ta Kudu sun kaddamar da hari a kan garin Bor, sa'o'i kafin cikar wa'adin tsagaita wuta.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fadan ya barke ne da asubahi kusa da sansaninta, kuma 'yan tawayen sun kwace wata babbar hanya mai mahimmanci.

Kakakin sojin gwamnati ya ce dakarunsu sun yi artabu da 'yan tawaye.

Shugaban Uganda, Yoweri Museveni ya yi barazanar daukar matakin soji idan har 'yan tawaye su ka ki zama a kan teburin sulhu.

Sai dai magudun 'yan tawaye, kuma tsohon mataimakin shugaban kasar, Riek Machar ya shaidawa BBC cewar zai tura tawaga wajen tattaunawar sulhu a kasar Ethiopia.

Shi kuma shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir ya kawar da yiwuwar kafa gwamnatin hadaka da jagoran 'yan tawaye Riek Machar, a kokarin kawo karshen rikicin kabilanci da ya haddasa mutuwar dubban mutane.

Karin bayani