An jinkirta sasanta rikicin Sudan ta Kudu

'Yan gudun hijira a Sudan ta Kudu
Image caption 'Yan gudun hijira a Sudan ta Kudu

An jinkirta tattaunawa tsakanin bangarorin dake yakar juna a Sudan ta Kudu -- abinda ya kawar da fatar kawo karshen tashin hankalin kabilancin da ya halaka mutane fiye da dubu daya.

A ranar juma'a an gudanar da tattaunawadaban daban tare da masu shiga tsakani a Addis Ababa babban birnin Ethiopia, kuma an shirya yin tattaunawar gaba da gaba a yau.

Kungiyar raya kasashen gabacin Afrika ta IGAD ce ke jagorantar tattaunawar.

Sakataren Kungiyar Mahboub Maalim ya shedawa BBC cewar nan ba da jimawa ba za a soma yin tarukan ido na ganin ido.

Wakilin BBC a Juba babban birnin Sudan ta Kudu, ya ce har yanzu ana ci gaba da gwabza kazamin fada.

Karin bayani