Somalia: Harin bam ya yi ta'adi

Image caption Birnin Mogadishu ya sha fama da hare-hare

Motoci a ƙalla biyu ne ɗauke da bama bamai suka tarwatse a wajen wani fitaccen Otel a Mogadishu babban birnin Somalia, kuma harbe-harbe sun biyo baya.

Jim kaɗan kuma daga nan wani bam din ya tashi yayin da motocin ɗaukar marassa lafiya da sojoji suke wurin.

Akwai dai rahotannin mutuwar mutane, to amma babu cikakken bayani.

Otel din na Jazeera dake kusa da filin jirgin sama na Mogadishu yana da farin jini ga 'yan siyasar Somalia.

An dai fatattaki kungiyar gwagwarmayar Islama ta Somalia Al-Shabaab daga Mogadishu a 2011, to amma suna ci gaba da kaddamar da hare hare.