An kashe mutane biyu a Iskandiriya

Zanga-zanga a Masar
Image caption Zanga-zanga a Masar

Ma'aikatar cikin gidan Masar ta ce an kashe mutane biyu a gwabzawar da aka yi tsakanin jami'an 'yan sanda da kuma magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi ranar laraba a Iskandiriya.

Ma'aikatar ta ce gwabzawar ta faru ne bayan wasu maci biyu da kungiyar ta 'yan uwa musulmai ta shirya wadda a makon da ya gabata aka ayyana ta a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Tun da farko 'yan sanda watsa barkonon tsohuwa da ruwan zafi akan daruruwan magoya bayan kungiyar da su ke zanga-zanga a kusa da ma'aikatar tsaron Alkahira.

Masar dai na fama da zanga-zanga tun bayan hambare gwamnatin shugaba Mohd Morsi a watan Yulin shekarar da ta gabata.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba