Boko Haram:Mutane 7,500 sun tsallaka Niger

Image caption Abubakar Shekau na mukarrabansa na Boko Haram

Kungiyar agaji ta kasa da kasa International Red Cross ta ce kawo yanzu mutane 7,500 ne su ka gujewa rikicin Boko Haram a Nigeria su ka tsallaka zuwa makwabciyar kasar Niger.

Mutanen da suka tsallaka sun hada da 'yan Nigeria da 'yan Niger da kuma 'yan Chadi.

Mutanen wadanda suke cikin mawuyacin hali sun yada zango ne a garuruwan Diffa, Toumour, Nguelkolo da kuma Chetimari.

Kakakin Red Cross a Jamhuriyar Niger, Oumarou Daddy Rabiou ya shaidawa BBC cewar suna tun daga watan Mayun 2012 zuwa yanzu suna bada tallafi ga dubban mutanen da suka gujewa yakin.

Rabiou ya kara da cewar "Yawancinsu mata ne da kananan yara, sannan kuma akwai 'yan Niger da Nigeria da kuma 'yan Chadi a cikin 'yan gudun hijirar".

Karin bayani