Tattaunawar sulhu kan Sudan ta Kudu

Image caption Dubban mutane sun rasa muhallansu

Tawagogin bangarorin biyu dake yaki da juna a Sudan ta Kudu, suna shirin fara tattaunawar sulhu a Addis Ababa, babban birnin kasar Ethiopia.

Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar, sun tura wakilansu zuwa birnin na Addis Ababa, amma kawo yanzu babu bangaren da ya amince ya tsagaita wuta.

A halin da ake ciki kuma, kungiyoyin agaji, sun ce dimbin fararen hula suna matukar bukatar agaji da matsugunni.

Yanzu haka dai mutane dubu 75 ne suke zaune a sansanonin da aka kafa a gabar kogin Nilu, bayan da suka tsallako cikin kananan jiragen ruwa, domin gujewa tashin hankali a garin Bor.

Bishop na Bor,Ruben Akurdit Ngong, wanda shi ma ya tsere daga garin, ya fadawa BBC cewa akwai gawawwaki da dama a warwatse a kan titunan garin na Bor.

Karin bayani