An samu Partrick Karegeya a mace a otal

Map din Rwanda
Image caption Map din Rwanda

'Yan sanda a Afrika ta kudu sun ce an samu gawar tsohon jami'in hukumar leken asirin Rwanda Patrick Karegeya a wani daki a otal din Johannesburg.

Mr Karegya ya nemi mafaka ne a Afrika ta kudu tun shekaru shida da suka gabata.

An dai tube shi daga mukamin sa na kanal ne bayan sun samu sabani da tsohon abokin kawance sa, Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame wanda ya zarge shi da hannu a harin ta'addancin da aka kai Kigali babban birnin kasar.

A cikin wata sanarwa, da jam'iyyar adawa a Rwanda ta fitar ta ce sha ke mr Karegeya aka yi, sai dai kuma ba bu wata cikakkiyar shaida.