Bincike kan kashe dan adawar Rwanda

Image caption Patrick Karegeya

'Yan sanda a Afrika ta Kudu sun kaddamar da bincike game da kisan wani jagoran 'yan adawa na Rwanda, Patrick Karegeya, wanda aka gano gawarsa a cikin wani dakin otel a birnin Johannesburg.

Kakakin Hukumar 'yan sandan ya ce binciken farko ya nuna cewa akwai kumburi a wuyan Mr Karegeya, kuma an gano wata igiya da wani tawul mai dauke da jini a cikin dakin otel din, abun dake nuna cewa mai yiwuwa an makure shi ne.

Mr Karegeya, wanda tsohon shugaban hukumar leken asirin Rwanda ne, ya gudu daga kasar ne, bayan da aka zarge shi da shirya makarkashiyar kifar da gwamnatin shugaba Paul Kagame a shekara ta 2006.

Jakadan Rwanda a Afrika ta Kudu, ya bayyana Mr Karegeya da cewa abokin gaba ne, amma ya musanta cewa gwamnatin Rwanda na da hannu a mutuwarsa.

Karin bayani