An yi kutsen shiga shafin Snapchat

Image caption Mutane miliyan 4.6 dake amfani da Snapchat

Masu satar shiga shafukan mutane a Intanet sun yi wa mutane miliyan hudu da dubu dari shida kutse a shafinsu na zumunta mai suna Snapchat.

Shafin intanet din da ya yi kutsen mai suna 'SnapchatDB' ya saka sunayen mutane da lambobin wayoyinsu wanda ya yi satar shiga.

Sai dai daga bisani an cire bayanan a intanet.

Kutsen na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wani kamfanin kasar Australia na tsaro a intanet, Gibson Security ya yi gargadin cewar manhajar Sanchat za ta iya fuskantar kutse daga masu satar shiga shafukan mutane.

Kamfanin Gibson Security ya ce babu hannunsa a kutsen: "Bamu da masaniya a kan abinda SnapchatDB ya yi".

Wadanda su ka yi kutsen sun bayyana cewar sun yi amfani da bayannan da Gibson Security ya bar inda suka samu nasara aikata laifin.

Karin bayani