Dakarun Italiya sun ceto 'yan ci rani 1000

Image caption Kasar Italiya ta kasance mashigar 'yan ci rani zuwa Turai

Rundunar mayakan ruwan Italy, ta ce mayakanta sun ceto 'yan ci-rani fiye da dubu daya a tekun Mediteranian a cikin sa'o'i 24 da suka wuce.

Helikoftocin rundunar ne suka hango wasu kananan jiragen ruwa, suna tangal-tangal, kuma makare da 'yan ci-ranin fiye da 800, amma mayakan ruwan na Italiya sun yi nasarar ceto su ba tare da wata matsala ba.

A wani al'ammarin na daban, an janyo wani jirgin ruwan dauke da 'yan ci-rani fiye da 200,har zuwa Sicily.

Rundunar mayakan ruwan kasar ta Italy dai ta yawaita sintiri tsakanin kasar da yankin Arewacin Afirka, tun bayan da daruruwan 'yan ci-rani suka mutu a gabar ruwan tsibirin Lampedusa a cikin watan Oktoba.

Karin bayani