An kaiwa Sarkin Jere hari a Kudancin Kaduna

Image caption Sarkin Jeren shine mijin Sanata Nenadi Usman

Rahotanni daga garin Jere dake karamar hukumar Kagarko a kudancin Kaduna na cewar an kaiwa Sarkin Jere, Dr Sa'ad Usman hari inda ya samu raunuka.

Bayanan da muka samu na cewar yanzu haka, Sarkin Jeren yana asibiti yana jinyar raunukan da ya samu.

Koda yake dai babu cikakken bayani game da abinda ya janyo matasa suka farma Sarkin, amma dai wasu majiyoyi sun ce lamarin nada nasaba da rashin jituwa tsakanin kabilun dake karamar hukumar ta Kagarko.

Kabilun dake zaune a Jere dai sune Hausawa, Fulani, Koro da kuma Gbagyi.

Karin bayani