Ba zan yi tazarce ba - Singh

Image caption Firaminista Manmohan Singh

Firaministan India, Manmohan Singh, ya sanar cewa ba zai nemi wa'adin mulki a karo na uku ba.

A wani taron manema labarai da bai saba yi ba, wanda shi na uku a cikin shekaru 10 da suka wuce, Mr Singh ya ce zai mika ragamar mulki ga wani sabon shugaba, idan har jam'iyyar ta Congress ta lashe zaben da za ayi a cikin watan Mayu mai zuwa.

Mr Singh ya ce "Rahul Gandhi, watau mataimakin shugaban jam'iyyar, yana da kwarewar da ake bukata domin zama dan takarar shugaban kasa, kuma ina fatan jam'iyyarmu za ta yanke wannan shawara".

Gwamnatin gamin gambizar Mr Singh dai tana fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa, amma wakilin BBC ya ce ana daukan Mr Singh din a matsayin mutumin da ya kawo sauye-sauyen tattalin arzikin da suka kai kasar ga samun cigaba.

Karin bayani