'Nigeria ba za ta sayar da matatun mai ba'

Image caption Matatun mai hudu kacal Nigeria ke dasu.

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya ce gwamnati ba ta da niyyar cefanar da matatun man fetur na kasar.

Kakakin fadar shugaban kasar, Reuben Abati a ganawarsa da manema labarai a Aso Rock, ya ce gwamnati ba ta bada umurnin a sayar da matatun man kasar hudu da take dasu a halin yanzu ba.

Abati yace "Gwamnati ba za ta sayar da matatun mai ba kuma fadar shugaban kasa ba ta bada umurni a kan cinikin ba".

A cikin watan Nuwamba ne aka ambato ministar dake kula da harkokin man fetur a kasar, Mrs. Diezani Alison-Madueke na cewar gwamnati za ta sayar da matatun man kasar.

Haka nan kuma a cewar Mr Abati, gwamnati ba tada niyyar kara farashin man fetur a kasar a cikin wannan shekarar.