Adadin masu kiba ya karu a kasashe masu tasowa

Masu fama da kiba ko taiba
Image caption Masu fama da kiba ko taiba

Wata cibiya mai zaman kanta dake Birtaniya ODI ta ce masu fama da kiba ko taiba a kasashe masu tasowa ya karu matuka, fiye da kasashe masu arziki.

A wani rahoto da ta fitar, cibiyar mai lura da ci gaba kasashen waje ta ce kusan mutane biliyan daya a irin wadannan kasashe na fama da kiba ko taiba tun daga shekara ta 2008.

Ta kuma ce adadin ya kara rubanyawa ne fiye da yadda aka gani a shekara ta 1980, yayin da a kasashen da suka ci gaba adadin ya karu ne zuwa miliyan 200.

Wani jami'in cibiyar ta ODI Steve Wiggins ya ce, karuwar adadin masu fama da kiba ko taibar a kasashe masu tasowar abin damuwa ne matuka.

Hakan kuma ya haifar da karuwar mutane masu fama da cututtukan sukari, sankara, hawan jini da ciwon bugun zuciya, da kara naunaya a fannonin tsarin kiwon lafiya a kasashen.

Rahoton ya karkare da cewa Yankunan Afirka ta Yamma, Gabas ta Tsakiya da Latin Amurka duka sun dara Nahiyar Turai yawan adadin masu fama da kiba ta taiba nesa ba kusa ba.