Kokarin sulhu kan rikicin Sudan ta Kudu

Image caption Shugabannin kasashen gabashin Afrika na son a dain zubar da jini

Bangarorin dake yaki da juna a Sudan ta Kudu sun soma tattaunawar sulhu a Addis Ababa, babban birnin kasar Ethiopia.

Suna ganawa da wakilan kasashen gabashin Afrika wadanda ke goyon bayan sulhun.

Nan gaba a yau (Juma'a) ne za a soma tattaunar keke-da-keke tsakanin gwamnatin Sudan ta Kudu da wakilan 'yan tawaye.

Dubban mutane ne suka mutu a rikici tsakanin dakarun Shugaba Salva Kiir da kuma na tsohon maitamakinsa Riek Machar.

Ofishin jakadancin Amurka a Sudan ta Kudu ya ce zai kwashe karin wasu ma'aikatansa daga kasar saboda karuwar tashin hankali.

Karin bayani