'Yan gudun hijira a birnin Bangui na cikin kunci

Yan gudun hijira a birnin Bangui Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Image caption Yan gudun hijira a birnin Bangui Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Kungiyar likitocin agaji ta Medicins Sans Frontier a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta ce al'amura a sansanin 'yan gudun hijira sun tsananta.

Al'amuran a sansanin dake filin saukar jiragen sama na Bangui babban birnin kasar sun kara tabarbarewa cikin kwanaki kadan da suka gabata.

Wata ma'akaciyar kungiyar ta MSF a sansanin Lindis Hurum ta shaidawa BBC cewa a cikin kwanakin baya bayan nan wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun bude wuta kai tsaye cikin sansanin da dakin shan magani, inda suka hallaka akalla yara uku.

Ta kuma ce akwai karancin abinci, ruwan sha a sansanin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fadan da ake gwamzawa a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na haifar da koma baya wajen taimakawa mutanen kusan miliyan guda da suka rasa matsugunasu.

Hukumar Lura da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akasarin mutane sun kauracewa gidajensu, yayinda mai magana da yawun kungiyar agaji ta Red Cross Nadia Bibsy ta shaidawa BBC cewa farmakin da ake kaiwa na haifar da cikas wajen bayar da agajin.

Kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai ta fada cikin rikicin addini tun bayan juyin mulkin da kungiyar musulmai ta Seleka suka jagoranta a bara.