Juba: Faɗa ya sake ɓarkewa

Rahotanni daga Juba, babban birnin Sudan ta kudu na cewa, ana can ana musayar wuta, lamarin da ya kawo karshen 'yar kwanciyar hankalin da aka samu a birnin.

Wasu dai na fargabar fada da ake yi a Sudan ta kudun zai iya rikidewa ya zama yaƙin basasa.

Ko ta ina dai a birnin na Juba ana jin karar manyan bindigogi, kuma hakan na faruwa ne yayin da ake tattaunawar sulhu tsakanin gwamnati da 'yan tawaye kasar Ethiopia.

Dubban mutane ne dai rikicin na Sudan ta kudu ya raba da muhallinsu, yayin da ɗaruruwan mutane suka mutu.

Wannan na faruwa ne yayin da aka soma tattaunawar sulhu a kasar Habasha.