Lebanon: Kwamandan Al-Qa'eda ya mutu

Image caption Marigayin dan asalin Saudiyya ne

Sojin Lebanon sun ce babban kwamandan ƙungiyar Al-Qa'eda a ƙasar, Majid Al-Majid ya mutu a tsare bayan da rashin lafiyarsa ta taɓarɓare matuƙa.

Ana dai yi masa magani ne a wani asubitin soji, sannan wani rahoton ya ce, ya samu matsalar mutuwar ƙoda ne.

Majed Al-Majed wanda ɗan ƙasar Saudiya ne shi ne shugaban ƙungiyar dake da alaka da Al-Qaida, mai suna baraden Abdullah Azzam, wadda ta ce ta na gudanar da hare haren bam.

Ƙungiyar ta ce, ita ta kai hari a ofishin Jakadancin Iran dake birnin Beirut.

An kama Majed Al-Majed a ƙarshen watan da ya wuce, kuma an tsare shi a wani wurin na sirri.