Ana gudanar da zabe a Bangladesh

Image caption 'Yan adawa sun kauracewa zaben Bangladesh

Ana gudanar da zabe a kasar Bangladesh duk da kauracewa zaben da 'yan adawa suka yi.

Wuraren kada kuri'u da dama an kona su a ranar jajiberin zaben na gama gari.

Jami'yyar adawa ta Bangladesh National Party BNP ta tursasa yin yajin aikin gama gari don hana yin zaben.

Firaministan kasar Sheik Hasina ta ture bukatun 'yan adawar na ta sauka daga karagar mulki don a gudanar da zabe mai adalci wanda kuma Hukuma ba ta gwamnati ba ta sa ido kan zaben.

Karin bayani