China ta nike ton shidda na hauren giwa

Hauren giwar da aka kwace
Image caption Hauren giwar da aka kwace

Gwamnatin China ta lalata sama da ton shidda na hauren giwa da ta kwace, a kokarin da cinikin hauren giwar ta haramtacciyar hanya.

An nike hauren giwar ne a garin Dongguan dake kudanci, kuma shi ne karon farko da aka yi hakan a kasar ta China ta bainar jama'a.

Dubban giwaye ne ake kashewa a Afrika a duk shekara, kuma ana kai galibin haurensu zuwa kasar ta China, inda ake mayar da su wasu kayan alatu, wadanda cikin daruruwan shekaru ake kallonsu da daraja a China.