Wani abu ya fashe a wata kotu a jihar Ribas

Image caption Gwamna Rotimi Ameachi na Ribas

Wani abu ya fashe a harabar babbar kotu dake Ahoada a jihar Ribas dake Kudu maso kudancin Nigeria.

Fashewar abin ya kawo tsaiko a sharia'ar da ake yi a kan batun shugabancin majalisar dokokin jihar ta Ribas da ake takaddama a kai.

Kakakin rundunar 'yan sanda jihar Ribas, DSP Ahmad Muhammad ya tabbatarwa da BBC afkuwar lamarin amma ya ce ba a samu hasarar rayuka ko jikkata sakamakon lamarin ba.

Ya kara da cewar jami'an 'yan sanda sun samu damar kwance wasu daga cikin abubuwan kafin su fashe.

Ana dai ja-in-ja game da shugabacin majalisar dokokin jihar ta Ribas inda aka samu mutane biyu ke kokawa a kan kujarar daya.

Karin bayani