An bukaci 'yan Fallujah su kori mayaka

Image caption Mayakan al-Qaeda sun karbe iko da Fallujah.

Pirai ministan Iraq Nouri al-Maliki ya bukaci mazauna garin Fallujah su kori masu tada kayar bayan masu alaka da al-Qaeda da suka mamaye birnin.

Ya ce idan mutanen su ka kori wadanda ya kira 'yan ta'adda, za su kare kansu daga harin soji.

Dubunnan mutane dai sun guje wa Fallujah domin kaucewa luguden bama-bamai da dakarun gwamnatin Iraq ke yi wa birnin.

A wani labarin kuma, bayanai daga birnin Ramadi dake lardi daya da Fallujah sun shaidawa BBC cewa yanzu birnin na karkashin ikon 'yan Sunni tare da hadin gwiwar 'yan sanda.