Mutane hudu sun mutu a rikicin Kaduna

Gwamna Mukhtar Ramalan Yero.
Image caption Gwamnan Kaduna ya tura jami'an tsaro yankin.

Kimanin mutane hudu ne suka rasu yayin da wasu suka jikkata a rikicin kabilanci da ya barke a jihar Kaduna da ke arewacin Nigeria.

Rikicin ya faru ne tsakanin kabilun Fulani da Attakar da ke karamar hukumar Kaura a kudancin jihar.

Wani mazaunin garin Abubakar Mukawo ya ce ricikin ya biyo bayan kashe wani bafulatani ne da aka yi. Bayan da 'yan sanda suka je kame sai matasa suka far musu inda suka sha da kyar.

Daga bisani kuma matasan sun kone rugagen Fulani tare da raunana mutane da dama.

Shugaban karamar hukumar Kaura Mr Kumai Badu ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya ce yanzu hankali ya kwanta bayan da jami'an tsaro suka fara sintiri a garin.

Karamar hukumar Kaura da ke makwabtaka da jihar Pilato na daga cikin yankunan dake fama da rikici a kudancin jihar Kaduna.