Tattalin arzikin Nigeria zai bunkasa

Image caption Tattalin arzikin Nigeria na bunkasa yayin da wasu ke fama da talauci.

A shekarar 2001 ne duniya ta fara zancen kasashen Bric, wato Brazil, Russia, India da China a matsayin kasashen da tattalin arzikinsu zai fi kowanne bunkasa. Masanin tattalin arzikin duniya Jim O'Neill ne ya yi hasashen inda yanzu kuma ya ce rukunin kasashen da ya kira "Mint" wato Mexico, Indonesia, Nigeria da Turkey sun dau hanyar zama jagaba kan habakar tattalin arziki. Ko me ye dalilinsa? Ga rahoton da ya yi wa BBC.

Na farko dai, baya ga yawan al'umma, adadin matasa masu jini a jika ya zarta na tsofaffi a cikin kasashen hudu daga yanzu zuwa akalla shekaru 20 masu zuwa. Hakan na nufin adadin wadanda za su iya aiki ya zarta wadanda ba za su iya ba.

Don haka in har Mexico, Indonesia, Nigeria da Turkey suka shiga taitayinsu za su iya samun bunkasar tattalin arziki cikin gaggawa irin wanda aka samu a China tsakanin shekarun 2003 zuwa 2008.

Kasashen na Mint na iya kafa kungiyar kansu kamar yadda na Brics suka yi. Hakan na iya sa Nigeria ta shiga kungiyar G20 ta kasashe masu karfin tattalin arziki kasancewar ragowar kasashen uku na cikinta.

A cewar ministar kudin Nigeria, Ngozi Okonjo-Iweala: "Lokacinmu na tafe. Kuma tabbas rashin Nigeria asara ce gare su."

Ba wuya Nigeria ta bada mamaki

Babban abin da na fi mai da hankali akai yayin ziyarata zuwa kasashen hudu shi ne yadda al'amura ke gudana a zahiri idan an kwatanta da hasashen masana.

Na dawo daga tafiye-tafiye na da tunanin cewa ba wani abu ne mai wuya ga Nigeria da Turkey su bai wa mutane mamaki ba, saboda mafi yawa an fi mai da hankali ne kan munanan abubuwan da suke faruwa irinsu aikata laifuka da rashawa a Nigeria da kuma tauye hakkin al'umma a Turkey.

Indonesia ce dai ban samu kwarin gwiwa ba. Kalubalen da suke fuskantar kasar sun kai yadda na zata kuma ban ga wani kokari da gwamnati ke yi na magance su ba. Hakika kasar na bukatar fadada tattalin arzikinta ta yadda za ta daina dogaro kan albarkatun kasa kadai.

Image caption Turkish Airline ne kamfanin jirgin saman da ya fi bunkasa a duniya.

A ziyarar da na kai Turkey, kamfanin Beko mai kera na'urorin amfanin cikin gida da Turkish Airline, kamfanin jiragen saman da ya fi kowanne bunkasa a duniya sun yi matukar burge ni. A Nigeria kuwa ko'ina na juya sai na ga abin burgewa.

Basirar da ke cikin kamfanonin Nigeria ta kayatar da ni sosai kuma har na dawo gida ina tunanin kamfanoni da dama da ya kamata na zuba hannun jari na a cikinsu.

A Mexico kuwa, matashin shugaban kasar da ministocinsa na bakin kokarinsu wurin yin garambawul ga tsarin ilimi, makamashi, kasuwanci da ma gwamnatin kanta.

Akwai kalubale

Sai dai kuma duk da haka kasashen na fama da kalubala wadanda ke razana masu zuba jari. Rashawa na daya daga cikin manyan matsalolin da suka addabi baki daya kasashen hudu.

A Nigeria, gwamnan babban banki Sanusi Lamido Sanusi ya ce cin rashawa bai cika hana bunkasar tattalin arziki ba. Kuma habakar tattalin arziki tare da inganta ilimi za su samar da kyakkyawan shugabanci da kuma tabbatar da gaskiya da adalci.

Wannan ra'ayi ne mai muhimmanci domin kuwa ga mutane da dama a kasashen Mint, rashawa na faruwa ne saboda sakacin da aka yi a baya amma ba za ta zama dalilin rashin ci gaba ba.

A Nigeria da Mexico, babbar matsala ita ce ta samar da wutar lantarki kuma kowacce daga cikinsu ta kaddamar da cikakken tsarin da in har za'a aiwatar da su za su kuwa bunkasar tattalin arziki.

Wani abin mamaki shi ne kimanin mutan miliyan 170 a Nigeria na amfani ne da adadin wutar lantarkin da mutane miliyan 1.5 ke amfani da ita a UK. Kusan kowane kamfani shi ya ke samar wa kansa da wutar lantarki. Kudin kuwa har sun zarta misali.

Image caption Mai kudin Afrika, Aliko Dangote na mamakin yadda Nigeria ke cigaba ba wutar lantarki.

"Ka san kuwa kasar nan ta na samun ci gaban tattalin arziki ne na kaso 7% ba tare da wutar lantarki ba?" Tambayar ke nan da mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya yi min.

Ina ganin tattalin arzikin Nigeria zai iya nunkawa cikin shekaru bakwai zuwa shida idan aka samar da wutar lantarki kurum.

A Indonesia, kasa ta hudu mafi girma a duniya, manyan matsalolinsu su ne rashin shugabanci da kayayyakin more rayuwa. Sai dai kuma akwai damarmaki da yawa a kasar.

Na hadu da mutumin da mutumin da ke gina shagon kayan daki na Ikea na farko a kasar, wanda ya ce min kaso daya cikin uku na mutane miliyan 28 da ke zaune a Jakarta za su iya sayen kayan kantin.

A Turkey, kalubalensu shi ne siyasa da kokarin cakudi musulunci da dabi'un kasashen Turai. Wadansu za su iya cewa ai akwai irin wannan kalubalen ma a Indonesia, amma ni da na je ban ga hakan ba. Domin kuwa a Jakarta tsarin rayuwar Turawa ya samu karbuwa sabanin Turkey.

Shin ko kasashen Mint za su iya shiga jerin kasashe 10 masu karfin tattalin arziki a duniya bayan Amurka, China, da sauran kasashen Brics da kuma Japan?

Ina kyautata zaton haka, koda yake za'a iya kwashe shekaru 30 kafin su kai wannan matsayi.