Angela Merkel ta karye a kugu

Image caption Angela Merkel ta karya kugu a wasan zamiyar kankara.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta karya wani kashin kugunta a wani hatsarin da ta yi a wasan zamiyar kankara a Switzerland.

Kakakin Ms Merkel, Steffen Seibert ya ce shugabar gwamnatin za ta kwanta jiyya tsawon makonni uku kuma za ta soke ziyarce-ziyarcen da ta shirya yi a lokacin.

Ya kuma ce ta samu raunuka a hatsarin da ya faru a tsaunukan Alps na yankin Engadine da ke gabashin Switzerland.

Ms Merkel, wadda yanzu ta ke iya dogara sanduna ta yi tafiya za ta jagoranci zaman majalisar ministocinta a karo na farko ranar Laraba.

Sai dai za ta ci gaba da gudunar da aikinta ne daga gida bayan da ta soke ziyarar da za ta kai Poland a makon nan kuma ba za ta karbi bakuncin sabon Pirai ministan Luxembourg wanda zai ziyarci Berlin ba.