Nijar na cigaba da tattaunawa da Areva

Masu zanga-zangar nuna adawa da Areva a Nijar
Image caption 'Yan Nijar da dama dai suna ganin cewa Areva na ci da gumin kasar

A jamhuriyar Nijar wata tawagar jami'an kamfanin Areva na Faransa tana tattaunawa a birnin Yamai da wasu jami'an gwamnatin kasar.

Wannan tattaunawa dai tana a matsayin wani bangare ne na cigaba da kokarin da bangarorin biyu ke yi na cimma sa hannu a kan wata sabuwar yarjejeniyar hakar Uranium a kasar ta Nijar.

Sai dai ya zuwa yanzu babu wasu cikakkun bayanai dangane da halin da ake ciki game da tattaunawar.

Kasar ta Nijar dai na fatan ganin ta samu riba fiye da wanda take samu a karkashin tsohuwar 'yarjejeniya ta shekaru 10, wadda ta kare a karshen watan Disamban da ya gabata.

Kamfani na Areva ya nemi gwamnatin Nijar din da ta bar shi ya cigaba da hako karfen na Uranium na tsawon watanni 3 a karkashin tsohuwar 'yarjejeniyar, amma gwamnatin ta yi watsi da wannan bukata.

Rahotanni dai na cewa tuni kamfanin na Areva ya dakatar da aikin hako Uranium din a Arlit dake Arewacin Nijar din.

Karin bayani