Nigeria na nasarar yaki da cin hanci

Image caption Najeriya na yunkuri kan yakar cinhanci

Ministan harkokin kasuwan ci a Najeriya ya bayyana cewa an samu ci gaba wajen magance matsalar cin hanci da rashawa da ake ganin shi ne babban kalubalen da ke addabar kasar.

Mr Olusegun Aganga ya shaidawa BBC cewa akwai matakai da gwamnatin Nigeria ta dauka na kokarin dakile cin hanci da rashawar.

Ya yi wannan jawabin ne bayan da kungiyar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta duniya Tranparency International a turance ta ce 'yan Najeriya na ganin cin hanci da rashawa na dada munana a kasar maimakon ya ragu.

Da dama daga cikin mutanen kasar na kokawa kan matsa lamba da jami'an 'yan sanda ke yi musu su ba su na goro.

Karin bayani