Senegal ta kama jirgin ruwan su na Rasha

Image caption Senegal na asarar CFA biliyan 150 duk shekara daga fashin kifaye da jiragen ruwan kasashen waje ke yi ma ta.

Senegal ta cafke jirgin ruwan Rasha bayan da ta zargi matukansa da yin su ba bisa ka'ida ba a lardin ruwanta.

Kakakin rundunar sojin Senegal Abou Thiam ya ce an kame 'yan Rasha 62 da 'yan Guinea-Bissau 20 bayan da sojin ruwa suka kai farmaki kan jirgin Rashan mai suna Oleg Naydenov.

Ministan albarkatun kifaye Haidar El-Ali ya ce kasar na shirin fito da wata doka da za ta bata ikon kwace duk wani jirgin ruwan kasashen waje da aka samu da laifin satar albarkatunta.

Mr Ali ya ce Senegal na iya cin tarar CFA miliyan 200 ga masu su ba izini amma za ta iya nunkawa Oleg Naydenov tarar saboda ba yau ya fara ba.

Ministan ya ce hukumar ci gaban kasashen duniya ta Amurka ta kiyasata cewa Senegal na asarar CFA biliyan 150 a kowacce shekara sanadiyyar fashin kifaye da jiragen ruwan kasashen waje ke yi ma ta.

Kawo yanzu dai kamfanin da ya mallaki jirgin ruwan bai ce uffan ba.