Sudan ta Kudu na tattaunawa kai tsaye da 'yan tawaye

Sojojin Sudan ta Kudu
Image caption Sojojin Sudan ta Kudu

Gwamnatin Sudan ta Kudu na gudanar ta tattaunawa kai tsaye a karon farko da 'yan tawayen da suka balle daga rundunar sojin kasar.

Bangarorin biyu sun hau teburin tattaunawa ne a Addis Ababa babban birnin Habasha.

A daya bangaren kuma, shugaban Sudan Omar Hassan Albashir na ganawa da Shugaban Sudan ta kudun Salva Kiir a Juba babban birnin kasar.

Ministan harkokin wajen Sudan din, Ali Karti ya ce kasarsa na tinanin tura sojojin hadin gwiwa tare da Sudan ta Kudu domin kare rijoyin mai na Sudan ta Kudun, wadanda 'yan tawaye ke kokarin kamewa.

A halin da ake ciki kuma, gwamnatin Sudan ta Kudun ta ce ta kulla 'yarjejeniyar tsagaita wuta da wani jagoran 'yan tawaye, David Yau Yau, wanda ke yaki da gwamnati a shekaru biyu da suka wuce.

Tun farko an nuna fargaba cewa Mr Yau Yau zai koma bangaren 'yan tawayen dake karkashin Riek Machar.

Karin bayani